Take a fresh look at your lifestyle.

π—žπ—ͺπ—”π— π—œπ—§π—œπ—‘ π—žπ—”π—₯-𝗧𝗔-π—žπ—ͺ𝗔𝗑𝗔 𝗬𝗔 𝗙𝗔π—₯𝗔 π—₯π—¨π—¦π—›π—˜ π—šπ—œπ—‘π—˜-π—šπ—œπ—‘π—˜ 𝗗𝗔 π—¦π—¨π—žπ—” 𝗦𝗔𝗕𝗔 π——π—’π—žπ—” 𝗔 π—žπ—”π—‘π—’

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 164

A daren ranar Asabar dinnan ce da misalin karfeΒ  ukuΒ  na dare kwamitin kar-ta-kwana karkashin jagorancin gwamnan jihar Kano da kwamishinan β€˜yansanda na jihar Usaini Gumel ya fara aikin rusa gine-gine da suka saba wa dokar jihar Kano.

 

Kwamitin ya fara ne da rushe gine mai hawa uku da aka gina mai shaguna 90 a katafaren filin sukuwar dawakin nan na Kano da ke yankin Nasarawa.

 

Idan dai ba a manta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi barazanar cewa zai rushe duk wasu gine-gine a wuraren amfanin al’umma da aka yi karfa-karfa aka kwace don son zuciya.

 

Wannan dai shine gini na farko da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta rushe tun bayan da ya karbi mulkin Kano a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar 2023.

 

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

Leave A Reply

Your email address will not be published.