Take a fresh look at your lifestyle.

Zanyi adalci wajan kafa majalisar zartarwar Jihar Neja. Gwamna Umar Mohammed Bago

Nura Muhammed,Minna.

0 135

Sakamakon yadda masu neman mukaman siyasa a jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ke tururuwar ganin sun sami shiga a dama da su a sabuwar gwamnatin jihar Neja, Gwamna Umar Mohammed Bago ya bayyana cewar zai  yi adalci wajan kafa majalisar zartarwa jahar.

 

Gwamnan ya bayana hakan ne a taron addu’oin godiya na samun nasarar kaddamar da Gwamna Umar Mohammed Bago a cucin St. Michael Catholic church dake garin Minna fadar gwamnatin jihar.

 

Gwamnan wanda matakamkin shi Yukubu Garba ya wakilta ya ce  za a yi adalci yayin zaban wadanda zasu kasance a gwamnatin, sai dai akwai bukatar a taya su da  addu’oi samun nasarar yin hakan.

 

A cewar sa ” zamu zabi wadanda suka chanchanci kasancewa da mu a gwamnatin, ina baku tabbacin cewar baza mu bi son zuciya ba wajan nadin illah chanchanta.”

 

Har ila yau gwamnan ya bukaci mabiya addinin krista da su gudanar da addu’oi samun nasarar kawo karashen matsalar tsaro a jahar da ma kasa baki daya.

 

Gwamna Umar Mohammed Bago ya kuma baiwa Yan jahar  tabbacin gwamnatin sa na sake dawowa da darasin CRK a makarantun jahar domin koyar da dabi’u nagari ga yara kanana.

 

Tun da farko a jawabin sa shugaban kungiyar kristoci na jahar Most Rev. Dr Bulus Dauwa Yohanna ya bukaci gwamnan da ya dawo da darasin CRK domin anfanar mabiya addinin a jahar Neja.

 

Rev. Bulus Dauwa Yohanna ya kara da cewar yin hakan zai taimaka wajan gyra tarbiya da dabi’un alumma musamma yara kanana.

 

Ya ce ” ana bukatar gyara  dabi’un alumma dole sai an samar da yanayin da zai taimaka masu wanda dawowa da  darasin CRK  na Daya daga cikin hanyoyin daukan gyra, zai taimaka wajan nunawa alumma yadda addini ke bukatar su su tafiyar da rayuwar  su na yau da kullum.”

 

A karashe Shugaban kungiyar kristocin ya bukaci hadin kan alummar jahar, ta hanyar  mantawa  da bambamce bambamcen adini da yare middin ana son a sami hadin Kai da  cigaba a jahar da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *