Take a fresh look at your lifestyle.

π—¬π—”π—žπ—œ 𝗗𝗔 𝗦𝗛𝗔π—₯𝗔π—₯ π—₯𝗒𝗕𝗔 π—”π—Ÿπ—›π—”π—žπ—œ Ne 𝗔 π—ͺ𝗨𝗬𝗔𝗑 π—žπ—’π—ͺ𝗔 – 𝗔𝗕𝗕𝗔 π—žπ—”π—•π—œπ—₯

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 163

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa yaki da sharar roba ko ta leda alhaki ne da ya rataya a wuyan kowa da kowa don tabbatar da samun muhalli mai cike da tsafta.

 

 

Da yake gabatar da jawabi a wajen taron tuni da ranar muhalli ta duniya a jami’ar Yusuf Maitama Sule gwamnan Kano ya bayyana Kano a matsayin gari da a baya yayi fice da kyakkyawan muhalli da a yanzu wannan daraja ta yi kasa dalilin sharar ta roba ko leda kamar yadda ta yi illa a wasu birane na duniya wacce ya ce sai kowa ya ba da tasa gudunmawa don yakar ta.

 

 

Taken taron ranar muhallin na bana dai shine β€œkawar da gurbata muhalli dalilin sharar roba ko leda.” A cewar Gwamna Abba Kabir cikin hanyoyi da za a samu mafita sun hadar da fadakar da al’umma kan illar sharar ta roba ko leda da ilimantar da al’umma kan kishin muhalli a shigar da kamfe na yaki da sharar a cikin al’umma da makarantu da maa’ikatu na gwamnati da karfafa gwiwar masu fasahar sake sarrafa sharar robar don amfanar jama’a.

 

 

Har ila yau gwamnan ya kara da cewa yakar sharar roba a Kano sai al’umma sun rage amfani da leda ko roba da za a yi amfani da ita sau daya kawai.

 

 

Taron dai bai kammala ba sai da gwamnan da mataimakinsa da wasu manyan jami;an gwamnati suka kaddamar da dasa bishiyu a jami’ar a hannu guda kuma ya kaddamar da kamfe na Tabbatar da tsaftar jihar Kano wato β€œKeep Kano Clean” a Turance a makarantar firamare ta Dandago da ke cikin birnin na Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *