Take a fresh look at your lifestyle.

CAN ta rabawa yan gudun hijira Kayayyakin abinci a jihar NejaNura Muhammed,Minna.

0 302

A kokarin ganin ta kawo sauki ga alummar jihar da suka shiga halin damuwa sakamakon matsalar tsaro a yankunan su, kungiyar kristoci ta CAN reshin jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta rarrabawa Yan gudun hijira Kayayyakin abinci a sansanin Yan gudun hijira dake kanana hukumomin Paikoro da shiroro a jihar.

 

Yan gudun hijiran dai sun kasance a makarantun faramare dake Gwada a karamar hukumar Shiroro inda Kuma na karamar hukumar Paikoro suka kasance a harabar cucin ECOWA.

 

Da yake mika Kayayyakin ga Yan gudun hijiran Shugaban kungiyar kristocin a jahar Neja Dr Bulus Dauwa Yohanna ya bukaci su da su cigaba da addu’oin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jahar da ma kasa baki daya.

 

Most Rev. Yohanna wanda ya sami wakilcin mataimakin sa Rev Ezekiel Ibrahim ya roke su da su karbi Kayayyakin da aka basu da hakuri inda ya ce kungiyar da ma mambobinta  zasu cigaba da yin  addu’oi domin su sami damar komawa yankunan cikin nasara.

 

Jagoran ya kara da cewar “batun rashin tsaro zai zo karshe da yaddar Ubangiji, Allah zai amsa addu’oin ku.”

 

Most Rev Yohanna ya Kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasa ransu yayin harin na yan bindiga da kuma yin addu’ar samun sauki ga wadanda suka sami rauni a hare haran yan ta’adda a wasu  kauyukan jahar Neja.

 

Kayayyakin da aka rabawa  yan gudun hijiran sun hada da shinkafa da wake da masara da taliyar indomie da man gyda da manja sai sabulun wanka da na wanki da gishiri da Kuma sinadarin dandano da sauran su.

 

Jagoran mujami’ar Peter and Paul Kafin Koro Rev Father Benedict John Adigizi shine ya karbi Kayayyakin a madadin Yan gudun hijiran, kana ya godewa kungiyar bisa namijin kokarinta  na ganin ta taimakawa alummar dake fama da halin damuwa a jahar Neja.

 

Rev Father Benedict ya ce akwai alumma da dama dake cikin damuwa a don haka wannan taimako zai rage masu wasu daga cikin damuwar.

 

Ya ce ” mutane da dama ne abun ya shafa inda wasu daga cikin su sun tafi wasu yankunan, Amma ganin jami’an tsaro a wasu daga cikin yankunan da abun ya shafa yanzun haka wasu sun fara komawa gidajen su, yadda ake ganin an fara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankunan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *