Take a fresh look at your lifestyle.

Tsofaffin ‘Yan Jarida Na Neman Magani Ga Kalubalen zamantakewa da Tattalin Arziki

0 449

Kungiyar tsoffin ‘yan jarida ta kasa (NALVEJ), reshen jihar Kwara a arewa ta tsakiyar Najeriya, ta koka da halin da al’ummar kasar ke ciki, tare da yin kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta samar da hanyoyin magance matsalolin tsaro da zamantakewar al’umma da ke addabar kasar. Kungiyar a cikin sanarwar da ta fitar a karshen taronta na wata-wata da ta gudanar a ranar Laraba ta yi Allah wadai da halin da ake ciki na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki da suka dabaibaye ‘yan Najeriya, musamman talakawa. Sanarwar ta samu hadin gwiwar shugaban kungiyar NALVEJ, Alhaji Tunde Akanbi da sakataren yada labarai, Alhaji Abdullahi Olesin. Kungiyar tsofaffin ‘yan jarida ta lura da hauhawar farashin kayayyakin abinci, da albarkatun man fetur, musamman kananzir da dizal, inda suka koka da yadda ci gaban ya yi illa ga ayyukan jaridu da gidajen rediyo da talabijin a fadin kasar nan. Yayin da ake korafin rashin aikin yi a kasar ya karu da kashi 33 cikin dari, kungiyar ta yi gargadin cewa tsadar dizal na iya kara dagula lamarin yayin da kayan aikin kafofin watsa labarai na iya rage karfin ma’aikatansu. “Farashin man dizal ya shafi tafiyar da yawancin gidajen jaridu, gidajen rediyo da kamfanoni, wanda hakan ya kai ga rufe gidajen watsa labarai da kayayyakin kasuwanci. “Yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ke yi, wani lamari ne mai tayar da hankali wanda ke bukatar kulawa cikin gaggawa. Kungiyar ta ce “Gwamnati na bukatar kudurin siyasa don shawo kan wadannan kalubale da sauran su.” NALVEJ ta jajanta wa talakawan Najeriya wadanda ke fama da matsalar rashin tsaro da kalubalen tattalin arziki, inda ya bukaci kowa da kowa da su marawa shugabannin kasar baya da addu’a a kokarinsu na neman mafita mai dorewa kan matsalolin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *