Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan jihar Neija ya jajantawa iyalan wadanda ‘Yan bindiga Suka Yi Garkuwa Da Su

Nura Muhammed,Minna.

0 102

Gwamnan Jihar Neija dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Muhammad Bago ya jajantawa iyalai da  kuma yan uwan wadanda harin Yan bindiga ya shafa a jihar.

 

Gwamnan ya kuma baiwa alummar jahar tabbacin gwamnatin sa na kula da hakkokin jami’an tsaro domin Kara masu kwarin gwiwar cigaba da samar da chikakken tsaro don kare  lafiya da dukiyoyin alummar jihar.

 

Gwamna Umar Muhammad Bago ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin nan a wani sako da sakataran yada labaran sa Bologi Ibrahim ya fitar aka rabawa manema labarai a garin Minna fadar gwamnatin jihar.

 

A cewar sa batun kula da jami’an tsaro musamma hakkokin su domin su sami zarafin kare rayuka da dukiyoyin alummar jahar Neija shine kan gaba a manyan ayyukan wannan gwamnatin.

 

Gwamna Umar Mohammed Bago ya Kara da cewar ” Ina son in baku tabbaci gwamnati na na kawo karshen wannan matsalar tsaron, Ina da yakin nan bada jimawa ba komi zai zama tarihi Saboda ganawar da na Yi da manyan hafsoshin tsaro kasar za a fara ganin alfanun sa kwanan nan.”

 

Gwamnan ya kuma Yi addu’ar fatan samun rahama ga wadanda suka rasa ransu a harin, kana yayi addu’ar ganin wadanda aka yi garkuwa da su sun dawo gidajen su lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *