Gwamnan jihar Neja ya Yi afuwa ga fursunoni 80 albarkacin ranar Demokradiya ta June 12.
Nura Muhammed,Minna.
Gwamnan Umar Muhammad Bago na jihar Neija dake arewa ta tsakiyar Najeriya ya yafewa mutane 80 dake zaman wakafi a gidan gyuaran hali domin bikin ranar demokradiya ta June 12.
Hakazalika Gwamnan ya amince da biyan Tara ta yadda fursunonin zasu sami yanci da Kuma zarafin hadewa da iyalan su.
A cikin wata sanarwa da ya fito daga ofishin sakataran gwamnatin jahar Alhaji Abubakar Usman Gawu ya ce Gwamnan ya Yi wannan karamcin ne domin bikin demokradiya na wannan shekarar da muke ciki, inda ya Yi anfani da damar da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi.
Abubakar Usman Gawu ya Kara da cewar majalisar dake bada shawarwari kan fursunonin ita ce ta baiwa Gwamnan shawarar hakan bayan nazari da ta Yi kan halayyar wasu fursunonin da aka amince da natsuwar su da Kuma yadda suka sauya dabi’ar su.
Har ila yau gwamna Umar Muhammad Bago ya shawarce wadanda aka saka da su kasance masu kishin jihar da Kuma kaucewa shiga duk wasu sabga da zasu Kara Maida su gidan wakafi.
Kungiyoyi kare hakkin bil’adama da dama ne suka Yi maraba da wannan matakin da Gwamnan jihar Neija ya dauka na yafewa fursunonin domin su sake shiga alumma.
Leave a Reply