Take a fresh look at your lifestyle.

π—¬π—¨π—‘π—žπ—¨π—₯π—œπ—‘ π—œπ—‘π—¨π—ͺ𝗔π—₯ π— π—¨π—¦π—¨π—Ÿπ— π—”π—‘ π—‘π—”π—π—˜π—₯π—œπ—¬π—” 𝗑𝗔 π—žπ—”π—ͺ𝗒 π—žπ—”π—₯π—¦π—›π—˜π—‘ π—™π—”π—¦π—›π—œπ—‘ π—ͺ𝗔𝗬𝗔 𝗔 π—žπ—”π—‘π—’

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

1 139

Inuwar Musulman Najeriya da hadin gwiwar jami’ar Al-Istiqama da Kungiyar Dalibai Musulmai a Najeriya reshen jihar Kano sun gudanar da taro da ya yi tattaunawa ta musamman a kan annobar kwacen waya ko fashin wayoyin hannu a tsakanin al’umma. Matsalar da al’umma ke ganin ta gawurta.

 

Taron dai ya samu halartar kwararru a fannin ilimin tsaro da manazarta kan aikata miyagun laifuka da masu yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da jami’an leken asiri da masu rike da sarautun gargajiya da malaman addini dana boko da ma masana kan halayyar dan Adam, baya ga sauran fannoni.Β  Alhaji Gidado Mukhtar shi ya jagoranci taron wanda Farfesa Salisu Shehu sakataren zartarwa na Inuwar Musulman Najeriya ya bayyana makasudinsa da zama “Tattaunawa ta musamman akan annobar kwacen waya “a kokari na neman mafita ga annobar da a cikin kankanin lokaci dalilinta aka kama daruruwan matasa, abin da ke zama babbar barazana ga zamantakewar al’ummar jihar Kano.

 

A cewar Farfesa Salisu Shehu fuska biyu za a iya kawo karshen matsalar fashin na waya; na daya ta hanyar amfani da karfi na jami’an tsaro, sannan na biyu a zauna a yi nazari kan matsalar a gano sabubbanta a yi mafani da hankali da nasiha da canza tunani da dabi’ar al’umma a dora al’umma kan turba mai kyau.

 

Dakta Maikano Madaki kwarraren masani kan ilimin aikata laifuka daga jami’ar Bayero ya gabatar da dogon jawabi kan abin da ake kira kwacen waya da yace tun daga Birtaniya shekaru kusan goma da suka gabata ake samun wannan dabi’a tsakanin matasa wadanda ba a raba su da shan miyagun kwayoyi, kuma abin takaici irin wayoyin da aka sata a can ana kawo su Najeriya musamman birnin Legas. Wannan dabi’a matasa a Najeriya su ma sun koya abin da ya kazanta kawo yanzu duk da kokari na jami’an tsaro. Hakan ya sa ake ganin jami’an tsaron na bukatar a kara masu yawa da kayan aiki irin na zamani, al’umma kuma su ci gaba daΒ  ba su hadin kai, sannan a bawa matasa kulawa da ta dace.

 

A bangaren kwamishinan β€˜yansanda na jihar Kano kuwa Usaini Gumel da ya samu wakiltar jami’i da ke magana da yawun β€˜yansanda na jihar ta Kano PPRO SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wannan matsala ta kwacen waya ba karama ba ce don haka suke aiki ba dare ba rana, kuma sannu a hankali saboda hadin kai da suke samu na al’umma suna samun nasara. Sai dai Kiyawa ya ja hankali na al’umma su guji daukar doka a hannu kasancewar hakan baya samar da mafita duba da yadda a Kudanci Najeriya yadda wasu ke daukar doka a hannu hakan bai samar da mafita ba, ana ci gaba da samun masu aikata laifuka.

 

A nasa tsokaci fitaccen malamin addinin Islama a Kano Malam Aminu Daurawa ya ce β€œMuddin a na so a kawo karshen kwacen waya sai al’umma ta amince cewa hakkin tarbiya abu ne da ya rataya a wuyan kowa a tallafa wa marasa galihu da marayu a taimaki zawarawa a samar wa matasa abin yi, uwa uba a samar da zauren sulhu da zai rika duba matsalolin tsaron al’umma tun daga matakin unguwanni don daidaita matsaloli na zamantakewa kafin ma zuwa ga β€˜yansanda .

 

Shima a nasa tsokaci Alhaji Ilyasu Mu’azu Sharada dagacin Sharada a jihar ta Kano ya bayyana cewa dole a rungumi matasa a kula da rayuwarsu sai an koma dabi’ar nan ta cewa da na kowa ne sannan za a ga daidai.

 

Muhammad Salisu Kabir shugaban kungiyar Musulman Najeriya reshen jihar Kano ya yi nasa tsokacin kan taron da cewa an samu masana da suka yi bayanai sosai kan matsalar satar wayar ta mahanga daban-daban, mataki na gaba shine a zauna don tattaunawa kan wadannan matsaloli da aka gano don daukar mataki na gaba, a fitar da shawarwari wanda za a mika wa hukuma a mika, wanda kuma za a ba wa kungiyoyi na al’umma a basu,Β  suma al’umma a sanar da su abin da ya kamata su yi ko su sani, duk dai don a samu mafita ga wannan matsala ta satar waya da sauran matsaloli don samun zamantakewa mai nagarta.

 

Uban taron kuma wakilin Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, Dan’Amar na Kano Aliyu Harazumi Umar a nasa jawabin a wajen taron ya jadda muhimmanci na rawar da masu sarautar gargajiya za su taka muddin ana son shawo kan irin wannan matsala ta fashin waya dama dangoginta kasancewar irin masu wannan sarauta su suka fi kusanci da jama’a.

 

Da dama cikin wadanda suka halarci taron da aka yi a shelkwatar ta Inuwar Musulman Najeriya da ke a Farm Centre a Kano sun nunar da cewa taro irin wannan da zai tattara kwararru a fannin Β tsaro da sauran masu ruwa da tsaki, ba kawai zai ba da mafita ga matsalar ta fashin waya ba har ma da wasu matsaloli na zamantakewa.

 

One response to “π—¬π—¨π—‘π—žπ—¨π—₯π—œπ—‘ π—œπ—‘π—¨π—ͺ𝗔π—₯ π— π—¨π—¦π—¨π—Ÿπ— π—”π—‘ π—‘π—”π—π—˜π—₯π—œπ—¬π—” 𝗑𝗔 π—žπ—”π—ͺ𝗒 π—žπ—”π—₯π—¦π—›π—˜π—‘ π—™π—”π—¦π—›π—œπ—‘ π—ͺ𝗔𝗬𝗔 𝗔 π—žπ—”π—‘π—’”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *