Take a fresh look at your lifestyle.

Tsohon kakakin majalisar, Gbajabiamila ya yi murabus Daga Shugabancin Majalisar Wakilai

0 99

Kakakin majalisar wakilai Rt. Hon. Tajuddeen Abbas ya ayyana kujerar tsohon kakakin majalisar Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, wanda ba ta kowa ba ce bayan wasikar murabus din shi a zauren majalisar ranar Laraba bisa bayanin kansa.

 

 

“A yau mun bayyana kujerar mazabar Surulere Legas 1 a matsayin wadda ba kowa akan ta bayan murabus din Gbajabiamila,” in ji Rt. Hon. Abbas bayan ya karbi wasikar kuma ya karanta wa mambobin.

 

 

Gbajabiamila ya bayyana a cikin wasikar murabus din shi da ya aike wa shugaban majalisar cewa zai dauki sabon matsayi a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (CoS) ga Shugaba Bola Tinubu.

 

 

Tsohon shugaban majalisar ya ci gaba da cewa zai daina zama dan majalisar wakilai ta 10.

 

 

KU KARANTA KUMA:Kun sanya ni zama Mafi kyawun Kakakin Majalisa, Gbajabiamila ya yabawa mataimakan sa

 

 

 

Gbajabiamila ya yabawa majalisar da al’ummar mazabar shi ta tarayya sakamakon nadin da shugaban kasa ya yi masa, ya kara da cewa yiwa majalisar hidima da al’ummar mazabarsa hidima ya zama babban abin girmamawa.

 

 

Gbajabiamila wanda aka rantsar a karo na 6 a ranar Talata ya mika takardar murabus dinsa ga kakakin majalisar, Tajudeen Abbas a zauren majalisar a ranar Laraba.

 

 

An zabe shi a majalisar don wakiltar mazabar tarayya ta Surulere 1 tsakanin 2003 zuwa 2023, tsohon dan majalisar ya yi aiki daban-daban a matsayin mai kare marasa rinjaye, shugaban marasa rinjaye, shugaban masu rinjaye da kakakin majalisa.

 

 

KU KARANTA KUMA: Majalisa ta 9: Kakakin Majalisa mai barin gado Femi Gbajabiamila

 

 

Kafin mika takardar murabus din nasa, Gbajbiamila ya gabatar da kudirin farko na muhimmancin gaggawa ga jama’a a zauren majalisa na 10 kan “Bukatar fara aiwatar da matakan da za a dauka don dakile bala’in ambaliyar ruwa mai tsanani da kuma shirya tsangwama don hana mummunan sakamako na zamantakewa da tattalin arziki ga ‘Yan Najeriya mazauna yankunan da abin ya shafa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *