Take a fresh look at your lifestyle.

Masana da Kwararru Sun Kafa Kungiya Don Ciyar Da Jihar Sokoto Gaba

Shehu Salmanu, Sokoto

0 167

Masana da kwararru a jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya sun yunkuro domin amfani da baiwar da Allah ya huwace masu ta hanyar samar da wata kungiya da za ta hada kan kwararrun domin ciyar da jihar dama kasa baki daya gaba ta hanyar baje kolin ƙwarewarsu.

Bukatar hakan ta taso ne duba da yadda ake samun ja baya wajen samar da kwararrun a bangarori na ci gaba da suka hada da kere-kere, fasahohi da dai sauransu.

Dukkanin kwararru a jihar masu shaida takardu na ilimin zamani da kuma masu ayyukan hannu a lunguna da sakunan jihar a yanzu zasu kasance karkashin inuwa daya domin inganta ayyukansu tare da gina yan baya wato matasa masu tasowa.

Injiniya Zayyanu Tambari Yabo da ke zama shugaban wannan sabuwar kungiyar ya yi ƙarin haske dangane da wannan ƙungiyar.
“Abun buƙata a nan shine samar da wani kyakyawan yanayi ga dukkanin masu sana’oin hannu a wannan jiha tamu domin samawa matasa da ayyukan yi gami da inganta sana’oin hannu da na garkajiya da ake ganin suna kokarin taɓarɓarewa”
Gudun yin tuya a manta da albasa akwai bukatar kama hannun dukkanin kwararrun da ake bukata a bangarorin rayuwa da suka hada da kanukawa, masu gyran wutar lantarki, masu walda, malaman jinya, likitoci, injiniyoyi, lauyoyi, makera, masunta, mahauta da sauransu ta hanyar bayar da goyon baya ga jaririyar kungiyar domin a gudu tare a tsira tare.

Kazalika, shugaban kungiyar ya mika sakon fatan hakan ga al’umar jihar ta Sokoto.
“Muna kira ga dukkanin wani mai ƙwarewa ko wace iri ce a jihar Sokoto da ya fito domin shiga a dama da shi wanda wannan shine manufar kafa ƙungiyar”
Masu sana’oin hannu na garkajiya da na zamani da kuma kwararru sune suka albarkaci taron da zummar mubayi’a gami bayar da cikakken goyon baya ga uwar kungiyar tasu.

 

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *