Kakakin majalisar dokokin jihar Benuwai, Mista Hyacinth Aondona-Dajoh, ya bukaci al’ummar jihar da su yi hakuri da sabuwar gwamnati, tare da ba su tabbacin za a kai ayyukan ci gaba nan ba da dadewa ba.
Shugaban majalisar ya yi wannan roko ne a wata ziyara da ya kai wa kungiyar ta Alia Alliance a Abuja ranar Alhamis.
Ya ce gwamnati za ta mai da hankali kan noma, kiwon lafiya, ilimi da samar da muhimman ababen more rayuwa domin biyan bukatun jama’a.
Aondona-Dajoh ya ce bangaren majalisar dokoki zai yi aiki kafada da kafada da bangaren zartaswa da na shari’a domin ciyar da jihar gaba.
Ya kuma bukaci kungiyar ta Alia da ta ci gaba da bayar da gudunmawar ci gaban jihar tare da shiga yaki da rashin shugabanci da rashawa.
“Na yaba da kokarin da kungiyar Alia Alliance ta yi na ganin jam’iyyar APC ta samu nasara a Benuwai, wanda shi ma ya kai ni matsayin kakakin majalisa.
“Ina kira ga kungiyoyi masu zaman kansu da daidaikun jama’a da cewa a matsayin ku da ku sanya ido kan wasu ayyukan gwamnati ku ba su rahotannin domin su kara yin aiki tare da tabbatar da inganci wajen yi wa jama’a hidima.”
A nasa martanin, babban sakataren kungiyar Mista Kelvin Dzeremo ya godewa shugaban majalisar bisa ziyarar da ya kai masa ba tare da bata lokaci ba, ya kuma taya shi murnar zabensa na shugabancin majalisar dokokin Benue.
Ya kuma bukace shi da ya mai da hankali da himma wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, ta yadda za a samu ci gaba a jihar.
Dzeremo ya ba da tabbacin cewa kungiyar za ta ci gaba da jajircewa wajen goyon bayan sa da gwamnatin jihar.
Leave a Reply