Gwamnan jihar Benuwai dake arewa ta tsakiyar Najeriya, Hyacinth Alia ya yi alkawarin baiwa gwamnatinsa goyon baya domin bunkasa wasanni a jihar.
Gwamnan, wanda mataimakin shi, Mista Samuel Ode, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Makurdi, a babban taron karawa juna sani na gasar kwallon kafa ta jihar Benuwai a shekarar 2023, wanda Ratels Sports Development Foundation, Abuja, (RSDF) ta dauki nauyi.
Ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga ci gaban wasanni domin hada kai da matasa, yana mai cewa za a farfado da gasar cin kofin gwamnan Benuwai a bana.
“Babu shakka babu wani abu da ya hada Najeriya kamar wasanni, musamman kwallon kafa,” in ji shi yayin da yake alkawarin cewa a matsayin gwamnati_ za su yi duk mai yiwuwa don bunkasa wasanni a jihar.
Ya yabawa wanda ya dauki nauyin gasar, Mista Paul Edeh, mallakin kungiyar kwallon kafa ta Naija Ratels, Abuja, saboda kasancewarsa jakadan wasanni na Benuwai.
Edeh ya ce gidauniyarsa, RSDF, tana daukar nauyin gasar a matsayin wata hanya ta mayar da hankali ga al’umma.
Edeh, wanda ya tsaya takarar shugabancin hukumar kwallon kafa ta jihar Benuwai (FA) a zaben na ranar Asabar, ya jaddada bukatar kara bunkasa kwallon kafa.
“Haka zalika gidauniyar Ratel a shirye take ta ba ‘yan wasan Benuwai guraben karatu don zuwa horon NIS,” in ji shi.
Mai bayar da agaji kuma jigo a harkar kwallon kafa mata a Najeriya ya yi alkawarin kawo sauyi a harkokin wasanni a Benuwai idan aka zabe shi a matsayin shugaba.
Kungiyar Zeal Minds FC ta doke Shinning Stars FC da ci 2-0 a Makurdi inda ta lashe gasar kwallon kafa ta jihar Benuwai.
Leave a Reply