Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Hon. Tajudeen Abbas ya bayyana alhininsa kan hatsarin kwale-kwalen da ya afku a jihar Kwara, wanda ya lakume rayukan mutane 104 a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya.
Ya ce ya ji takaicin yadda aka yi asarar rayukan ‘yan uwanmu sama da 100 a wannan mummunan lamari da ya faru a karamar hukumar Patigi.
Ya ce labarin faruwar al’amarin ya yi matukar tayar da hankali kamar yadda abin takaici ne, yana mai cewa dole ne a kauce wa faruwar hakan domin ceto rayukan ‘yan Najeriya.
“Zuciyata na zubar jini. Na ji zafi da bacin rai da labarin hatsarin jirgin ruwa a Kwara. Rayukan ‘yan Najeriya 104 na da matukar daraja, amma mun rasa su haka nan a cikin dare daya. Lamarin ya yi yawa. Dole ne mu kiyaye daga irin waɗannan abubuwan a nan gaba. Dole ne a dauki matakan da suka dace don hana faruwar hakan. Tunanina da addu’a na tare da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu yayin wannan lamari,” in ji kakakin majalisar Abbas.
Ya mika sakon ta’aziyyarsa ga jama’a da gwamnatin jihar Kwara bisa asarar rayuka da aka yi, wanda ya bayyana a matsayin abin bakin ciki.
Kuma ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, tare da yi wa wadanda suka samu raunuka fatan samun sauki cikin gaggawa.
Leave a Reply