Take a fresh look at your lifestyle.

Kanfani Ya Bukaci Shigar Da Mata Harkokin Noma A Najeriya

0 128

Wani kamfanin noma mai suna Value Seed Limited yana ba da shawarar shigar da mata a harkar noma a Najeriya don inganta aiki da kima.

 

Shugaban kamfanin, Sir George Zangir ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan gabatar da jawabinsa a taron masu ruwa da tsaki na kungiyar AGRA a jihar Kaduna.

 

Zangir ya yi kira ga mata manoma da su yi amfani da damar da suke da ita a masana’antar don tasiri mai kyau ga al’umma.

 

“Taron na yau shine karo na farko a shekarar 2023 kuma yana da mahimmanci a gare mu mu sa ido don tattauna ci gaban da aka samu, darussan da aka koya da kuma damar da ke gabanmu yayin da muke kokarin inganta rayuwar mata a fannin noma”.

 

A cewarsa, shirin hadin gwiwar mata da aka fara a shekarar 2022 zai ci gaba har zuwa shekarar 2024, wato tsawon shekaru uku, da nufin inganta noman farko da kuma karfafa gwiwar mata manoma a kasar nan.

 

Har ila yau, Shugaban Project na kamfanin, Idoko Gabriel Samson ya bayyana cewa, shirin na AGRA Gender consortium yana gudana a lokaci guda a jihohi biyu na tarayya, Neja da jihar Kaduna.

 

Da aka tambaye shi kan zaben jihar Neja da Kaduna, ya bayyana cewa jihohin da aka zaba sun zama masu jan hankali a wannan aikin saboda talauci da yawansu, don haka akwai bukatar a inganta rayuwar mata manoma domin amfanin al’umma.

 

Samson ya kara da cewa an yi niyya ga adadin mata da suka dace don aikin hadin gwiwar jinsi na AGRA a jihohin biyu da aka ambata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *