An yi kira ga shugabannin yankin Arewacin Najeriya da su hada kai da juna domin ciyar da yankin gaba.
Jigo a jam’iyyar APC reshen jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya kana tsohon maitaimakawa gwamnan jihar Borno kan harkokin siyasa a zamanin mulkin Kashim Shatima Hon Yusuf Adamu ne ya bada wannan shawarar yayin zantawarsa da Muryar Najeriya.
Dan siyasan ya ce muddun shugabannin da Allah ya huwacema Arewacin Najeriya suka hada kai a wuri guda, to kuwa hakika za a samu gagarumin ci gaba a yankin dama kasar baki daya.
A cewarsa, “tuni magabata suka sanya kasar a kyakyawan tsari na cigaba, sai dai abun takaici ne, yadda wadansu kan juyama wannan tsari baya, wadda yin hakan ba zai haifar da da mai ido ba ga yankin dama kasar baki daya, ya kuma jaddada kira ga jagororin Arewacin Najeriya da su baiwa mataimakin shugaban kasar Kashim Shatima goyon baya domin yayi amfani da gogerwarsa ta fuskar ci gaban kasa ta hanyar farfado da masana’antun da tuni suka durkushe.
Bugu da kari, Honorobul Yusuf Adamu ya hori matasa da su kasance masu rungumar sana’oin hannu domin cin moriyar tarin albarkatun karkashin kasa da sauran ma’adanai da Allah ya azurta Najeriya da su, kana ya bukaci gwamnati da ta kasance mai bibiya akan shirye-shiryen da ta tanadar domin taimakawa masu kananu da matsakaitan sana’oi musamman ma dumbin matasa dake kasar.
Ak
Leave a Reply