Bikin Babbar Sallah: Gwamnan Jihar Katsina Ya Bukaci Musulmi Su Yima Najeriya Addu’ar Zaman Lafiya
Kamilu Lawal,Katsina.
Gwamnan jihar Katsina dake arewa maso yammacin najeriya, Malam Dikko Umaru Radda yayi Kira ga al’ummar musulmi a jihar da sauran sassan kasar su saka kasar a cikin addu’o’in su na wannan lokaci na babbar Sallah domin samun hadin kai a tsakanin al’ummomi mabiya addini da kabilu daban daban da Allah ya azurta kasar dasu
Ya kuma bukace su da su dauki junansu a matsayin abu daya ba tare da nuna wani banbancin addini ko kabilanci a tsakanin su ba, domin samun rabauta daga Allah mahaliccin kowa a wannan lokacin sadaukarwa na babbar Sallah layya
A sakon sa na babbar Sallah, mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran sa, Ibrahim Kaula muhammad, Gwamna Radda ya kuma bukaci al’ummar musulmin da su saka shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu da gwamnoni da sauran shugabanni a cikin addu’a a wannan mahimmin lokaci da shugabannin ke ta kokarin ganin sun fitar da kasar daga kalubalen da take fuskanta domin sake gina ta
Ya kuma bukaci al’ummar musulmin da su kalli lokacin babbar sallar fiye da wani lokaci na shagulgula da yanka dabbobin layya domin rabawa ga dangin su kadai, yana mai kira garesu da su fadada ranar wajen kokarin kyautatawa hadi da tallafama gajiyayyu da marasa karfi tare da wadanda matsalar tsaro ta rabo da yankunan su domin faranta masu
Gwamna Radda ya kuma bukaci al’ummar musulmin da cewa” Ku yi koyi da Annabi Ibrahim wanda ya nuna tsantsar biyyayyar sa ga mahaliccin mu Allah SWT tare da bin umarnin sa na amincewa ya yanka dan sa Annabi Isma’il
Gwamnan ya bukace su da su kara jajircewa wajen hakikanin bautar Allah tare da dagewa wajen bin dokoki da ka’idojin addinin musuluncin domin samun kyakkyawan sakamako anan duniya da kuma ranar gobe kiyama”, inji Gwamna Radda.
Kamilu Lawal.
Leave a Reply