Take a fresh look at your lifestyle.

FCDO Ta Kashe Dala Milyan 109 Kan Ilimin Mata A Arewacin Najeriya

Hadiza Halliru Muhammad, Sokoto

0 852

Hukumar Kungiyar Rainon Kasashen Ingila FCDO tare da hadin gwiwar Asusun  kula da kananan yara na majalisar Dinkin Duniya ( UNICEF), ta kashe Dala Milyan Dari da Tara (109) kan ilimin ya’ya mata a jihohi shida dake arewacin Najeriya, da suka hada da Zamfara, Niger, Kano, Bauchi da kuma Katsina.

Majanajar offishin FCDO A Jihar Sokoto, Dr Miriam Mareso ce ta bayyana hakan a wani Taron manema labarai da ya guda a Jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Najeriya.

Manufar shi ne kara yawaitar yara mata a makarantu musamman la’akari da kididdigar da ta nuna cewa an bar jihohin a baya wajen ilimin mata.

Najeriya na da yawan yara milyan goma da rabi wadanda ba sa zuwa makaranta.

Taron tattaunawa da yan jaridun a Sokoto, ya kuma tunasar da su rawar da za su taka domin tallafawa kokarin da Hukumar ta  FCDO da gwamnatoci a matakai mabanbanta ke baiwa yara mata cikakkiyar damar samun ililmi musamman a mataki na farko.

Abokiyar aiki Hadiza Halliru Muhammad na daga cikin yan jaridun ga kuma rahoton da ta hada mana daga Sakkwato:

 

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *