A ranar Lahadi Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya ‘yan was an tseren da suka wakilci Najeriya a wasannin kasashe renon ingila da aka gudanar a birnin, Birmingham 2022.
Shugaban ya bi sahun sauran Miliyoyin ‘yan Najeriya masoya wasannin motsa jiki murnar rawar gani da suka nuna a gasar da kimanin ‘yan wasannin tsare dubu biyar suka halarta daga kasashe 75, domin gasar lashe kyautuka 280.
Da yake jinjina wa tawagar ‘yan wasan tseren Najeriya,Shugaban ya yaba da irin rawar gani da ‘yan Najeriya 94 a matsayin sun a jakadai na gari da suka daga Tutar Najeriya a wasannin Tara,daga karshe aka karrama su da kyaututtuka tare da annuri a fuskokin su a lokacin da ake rataya musu.
LADAN NASIDI
Leave a Reply