Afirka ta Kudu ta fada jiya Alhamis cewa, taron na BRICS zai gudana kamar yadda aka tsara, a daidai lokacin da ake kyautata zaton za a kai shi kasar Sin domin bai wa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin damar halartar taron.
A watan Maris ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta tuhumi shugaban na Rasha da yin garkuwa da yaran Ukraine, kuma an bayar da sammacin kama shi.
Afirka ta Kudu za ta karbi bakuncin taron BRICS daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta a Johannesburg.
A ranar Talata, ministan harkokin wajen Afirka ta Kudu ya ce babu wani tabbaci na halartar daga Putin.
Ana sa ran shugabannin kasashen China da Brazil da Indiya za su halarci taron.
Kasashen yammacin duniya sun kai wa Afirka ta Kudu hari saboda matsayar ta na tsaka-tsaki kan rikicin Ukraine.
A cikin watan Mayu, jakadan Amurka a Afirka ta Kudu ya zargi kasar bakan gizo da lodin makamai ko fasahohin da ke da alaka da wani jirgin ruwan Rasha da ya makale a sansanin sojojin ruwa na garin Simon.
Shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya musanta wadannan zarge-zarge, wanda tun daga lokacin ya bude bincike kan lamarin.
L.N
Leave a Reply