Kashi na farko na daliban jihar Kano da suka ci gajiyar tallafin karatu na kasashen waje ana sa ran za su fara tashi a watan Satumba na wannan shekara.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a gidan gwamnati ranar Asabar lokacin da ya karbi bakuncin mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero da ‘yan majalisar masarautun da suka kai gaisuwar Sallah ga Gwamnan.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Hisham Habib ya fitar, gwamnan ya ce wannan ci gaban na daga cikin kokarin da ake yi na aiwatar da manufofin gwamnatin sa na neman gurbin karatu a kasashen waje.
Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa bisa fifikon da ake bukata a bangaren ilimi.
“Gwamnati ta shirya bude cibiyoyi 20 da gwamnatin da ta shude ta rufe, da makarantun Islamiyya da kwalejojin fasaha da ke lungu da sako na jihar da nufin samar da ingantaccen ilimi ga matasa a jihar,” inji Gwamnan. .
Ya godewa Sarkin yayin da ya yaba da rawar da sarakunan gargajiya ke takawa a matsayin masu kula da al’adu da yada zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban al’umma.
Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya ce ya ziyarci gidan gwamnati ne domin yi wa gwamna barka da Sallah tare da yin amfani da wannan damar wajen yin kira da a samar wa manoma taki a farashi mai rahusa da bukatar yakin noman itatuwa da hako rijiyoyin burtsatse.
Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta gayyaci masu zuba jari don bunkasa tattalin arzikin jihar.
Ya godewa Gwamnan bisa nada dan masarautu, Dr Abdullahi Baffa Bichi a matsayin sakataren gwamnatin jihar Kano.
L.N
Leave a Reply