Gwamna Umaru Bago na jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ya rusa hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar.
Hakan ya fito ne ta wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Abubakar Usman, ya fitar ranar Lahadi a Minna, babban birnin jihar.
Rushewar, in ji shi, zai fara aiki daga ranar 29 ga Mayu 2023.
Sanarwar ta kara da cewa, “An umurci mambobin hukumar da su mika dukkan kadarorin gwamnatin jihar da ke hannunsu ga babban darakta nan take.”
A halin da ake ciki dai, za a iya tunawa a ranar 27 ga watan Satumban 2022 ne Majalisar Dokokin Jihar Neja ta kori Shugaban Hukumar NSIEC, Alhaji Baba Aminu, bisa zargin rashin da’a.
NAN/L.N
Leave a Reply