Gwamna Ahmadu Fintiri ya haramta yankewa da kona kututturan itatuwa da nufin yin gawayi a jihar Adamawa. Gwamnan ya bayyana cewa dokar da ta haramta sare itatuwa da kuma yin amfani da kututturan bishiya wajen yin gawayi domin girki za a yi amfani da su sosai.
Tun da farko Gwamna Fintiri ne ya bayar da umarnin a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya da suka kai ziyara Yola fadar gwamnatin jihar domin yi masa mubayi’a a fadar gwamnati, sai kuma ‘yan majalisar dokokin jihar.
Shugabar majalisar, Bathiya Wesley, ta jaddada wajibcin da ya wajaba a kan ‘yan majalisar su tabbatar da dokar da ta haramta yanke bishiyu.
“Mun cimma matsaya mai karfi na cewa kada a sare bishiyu ko kuma samar da gawayi. Ana sa ran dukkanmu za mu taka rawar gani wajen ganin an aiwatar da dokar hana sare itatuwa da ba mu aiwatar da ita ba a yanzu. Na fada wa sarakunan gargajiya a lokacin da suka zo.
“Dole ne dukkanmu mu yi abin da ya kamata mu yi ta bangarenmu ta wannan hanyar. Dole ne mu karfafa wa jama’armu gwiwa su koma hanyar da za ta dore a madadin gawayi.”
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa ta yanke shawarar hana sare itatuwa musamman don konewa da kuma yin gawayi saboda an gano sare dazuzzuka da ke haddasa ambaliyar ruwa mai yawa a fadin jihar.
“Mun ga wuraren da ba a taba samun ambaliyar ruwa ba a yanzu ana yawaita ambaliya, suna lalata gonakinmu, gidajenmu, da dukiyoyi masu muhimmanci,” in ji shi.
Agro Nigeria/L.N
Leave a Reply