An saki Bishop na Katolika na Nicaragua Rolando Alvarez daga gidan yari wanda ke nuna yiwuwar sauyi a yunkurin da gwamnati ta dauki tsawon lokaci tana murkushe Cocin Katolika.
Wata majiyar diflomasiyya ta ce ana ci gaba da tattaunawa tsakanin gwamnati da limaman darikar Katolika na kasar kan makomar Alvarez, kuma shugaban cocin ya kasance a harabar cocin Katolika da ke babban birnin kasar.
Majiyar wadda ta ki a bayyana sunan ta, ta kara da cewa tattaunawar ta hada da yiwuwar korar Bishop din daga kasar Amurka ta tsakiya ko kuma a tura shi gudun hijira.
Gwamnati ba ta mayar da martani nan take ba kan bukatar yin tsokaci kan sakin Alvarez bayan sa’o’in kasuwanci na yau Talata.
Karanta kuma: Nicaragua ta zargi Cocin Katolika da laifin karkatar da kudade
Majiyar ta ce idan Bishop din ya ki barin kasar, za a iya mayar da shi gidan yari.
Alvarez, Bishop na karkarar Matagalpa kuma fitaccen mai sukar shugaban kasar Daniel Ortega, an daure shi a shekarar da ta gabata, kuma a bana an yanke masa hukuncin daurin shekaru 26 a gidan yari bisa zargin cin amanar kasa bayan ya ki a kore shi zuwa Amurka.
Alakar da ke tsakanin gwamnatin Nicaragua da fadar Vatican ta katse a bana bayan Paparoma Francis ya yi wa gwamnatin Ortega ba’a a matsayin mulkin kama-karya.
Tushen rikicin dai ya samo asali ne tun shekaru biyar da suka gabata, lokacin da gwamnatin kasar ta kira shugabannin coci-coci da su shiga tsakani a zanga-zangar kin jinin gwamnati da ta rikide zuwa tarzoma tare da mutuwar mutane sama da 300.
L.N
Leave a Reply