Take a fresh look at your lifestyle.

Zamu Gina sansanin alhazan jihar Neja na dindindin- Gwamna Umar Mohammed Bago

Nura Muhammed,Minna.

0 305

Hukumar jin dadin alhazan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta yabawa Gwamnan jihar Umar Mohammed Bago bisa karamcin da ya nunwa alhazan jihar a kasa Mai tsarki.

 

Shugaban hukumar Alhaji Muhammad Awwal Aliyu shine ya bayyana hakan  ta bakin Mai magana da yawun hukumar jin dadin alhazan jihar Hassan Danladi, inda ya ce Mai girma Gwamnan ya baiwa alhazan su 3,710 kudi a lokacin da ya ziyarci su a Muna.

 

Shugaban hukumar ya Kara da cewar wannan karamcin da Gwamnan ya nunawa Yan jihar yayi ne bisa Karin Kansa domin rage masu irin damuwa da suka shiga na rashin kudi da wasu alhazan suka shiga.

 

Alhaji Muhammad Awwal Aliyu ya ce bayaga alhazan Gwamnan ya Kuma baiwa jami’an hukumar dake hidima da alhazan kudi Wanda hakan ya karawa jami’an kwarin gwiwar cigaba da ayyukan su na kula da Kuma Kara hidimtawa alhazan jihar Neja.

 

A jawabin sa ga alhazan bayan Mika masu kudaden Gwamnan Umar Muhammad Bago ya ce gwamnatin jihar zata Kara inganta hanyoyin da zasu taimakawa duk wani manuniyaci da ya fito daga jihar Neja a aikin hajjin gaba.

 

Gwamnan ya Kuma yi alkwarin Gina sansanin alhazan na dindindin da zai taimakawa Maniyata samun natsuwa.

 

Gwamnan ya ce ” Zamu himmatu wajan ganin alhazan jihar Neja na tashi daga Minna inda za a tabbatar da an inganta filin jirgin saman Minna ya kasance abun alfahari.”

 

Nura Muhammed,Minna

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *