Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnan Jihar Borno Ya Bai Wa Manoma Motoci 80

0 110

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya saki motocin bas guda 80 da motocin daukar kaya domin jigilar manoma daga yankunansu zuwa gonaki kyauta.

 

A cewarsa, “Ina so in roke ku da ku ba da cikakken goyon baya da hadin kai ga sojojin Najeriya. Suna nan don su kare ku.”

 

Sai dai a cikin motocin guda 80, motocin alfarma guda 50 na karkashin kulawar hukumar Borno Express ta jihar, yayin da jihar ke daukar hayar motocin daukar kaya guda 30.

 

“Muna nan da ba da tallafa wa manoma; za ka ga dubbansu sun taru kuma za su kai 100,000. Muna yin haka ne saboda cire tallafin man fetur da akayi, wanda duk da cewa yana da fa’ida na dogon lokaci, amma ya kara tsadar sufuri.”

 

Ya bukaci manoman da su bai wa sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro hadin gwiwa da aka girke a kan tituna domin kare ‘yan kasa, ciki har da manoman da ke zuwa gonakinsu da ke wajen birnin.

 

KU KARANTA : Tallafi: Shugaban Ribas LG ya baiwa manoma 50

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *