Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gaggauta Magance Matsalar Tsaro A Jihar Katsina.
Abdulkarim Rabiu, Abuja
Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta bullo da wani sunturin hadin guiwa na rundunar tsaro domin kakkabe ‘yan bindiga, da lalata sansanonin su ta yadda mamona za su damar komawa gonakinsu.
Wannan ya biyo bayan amincewa da wani kudiri da ya bukaci magance hare-haren ‘yan bindiga da ake kaiwa kauyukan kananan hukumomin Dustin-Ma da Kurfi a jihar Katsina dake Arewa maso yammancin Najeriya, wanda wani dan majalisa daga jihar, Aminu Balele Kurfi ya gabatar a zauren majalisar.
Dan majalisar ya bayyana cewa, a ranar 12 ga watan Yunin 2023, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wasu al’ummomi bakwai a cikin kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma na jihar Katsina, wanda ya yi sanadiyyar jikkata da mutuwar wasu da dama da ba su ji ba ba su gani ba.
Ya ci gaba da cewa, ayyukan ‘yan ta’adda da ake yi a yankunan biyu da sauran al’ummomin da ke makwabtaka da kananan hukumomin Safana da Batsari ya janyo kakaba haraji akan manoma akai-akai kafin a ba su damar shiga gonakinsu domin yin noma, wanda rashin biyan harajin ke jefa su cikin hadarin rasa dabbobinsu ga barayin tare da fasa shagunansu da masu garkuwa da mutane ke yi.
Har ila yau Hon. Balele ya bayyana damuwa kan yadda hare-haren da ‘yan bindigar ke kaiwa ya haifar da raguwar amfanin noma, wanda hakan ke kara ta’azzara matsalar karancin abinci a yankunan da lamarin ya shafa.
“Yawancin matasan da ke yankunan da abin ya shafa za su iya fuskantar rashi ko karancin
samun kudin shiga wanda hakan yana kara tabarbarewar rayuwar matasa” In ji Hon. Balele
Majalisar ta Kuma bayyana damuwa cewa yayin da damuna ta fara kankama, ‘yan fashin daji na barazana ga manoman yankin
su biya harajin da aka sanya ko kuma a yi garkuwa da su don neman kudin fansa mai yawa.
Kazali, Dan majalisar ya bayyana cewa akwai bukatar a dauki tsauraran matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma kamar yadda kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, na 1999 da aka yi wa kwaskwarima ya tanadar
Da take amincewa da kudirin majalisar ta yanke shawarar kafa wani kwamiti na wucin gadi don gayyatar manyan hafsoshin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda, da Darakta Janar na hukumar tsaro ta farin kaya don gudanar da bincike kan zargin sakacin da hukumomin tsaro ke yi na shawo kan matsalar ‘yan fashin daji a Jihar.
Abdulkarim Rabiu.
Leave a Reply