Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya tabbatar wa masu zuba jari na kasashen waje domin kare lafiyar jarin da suke zuba a Najeriya, inda ya jaddada kudirin gwamnatin Tinubu na samar da ingantaccen yanayin kasuwanci ga masu zuba jari na kasashen waje a kasar.
Sanata Akpabio ya bayyana haka ne a ofishin sa yayin da ya karbi bakuncin Jampur International, karkashin jagorancin babban jami’in kamfanin, Mohanmed Shafiq.
A cewar shi, “Ina maraba da ku a madadin Majalisar Dattawan Tarayyar Najeriya. Najeriya tana da aminci sosai kuma a shirye take ga masu zuba jari. Ina sane da cewa kun riga kun saka hannun jari a Najeriya a fannin hakar ma’adinai, wutar lantarki da kasuwanci. Na gode da daukar ‘yan Najeriya aiki a kamfanoninku”.
Sanata Akpabio ya yi nuni da cewa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na sanya farashi guda na musayar kudaden waje, wani yunkuri ne da gangan da gwamnatin ta yi na kara tabbatar wa masu zuba jari na kasashen waje tsaron jarin su a ko’ina a Najeriya.
“Gwamnatin da ke ci a yanzu ta samu damar daidaita farashin musaya na kasashen waje ta hanyar da taga daya kacal. Zuba hannun jari a Najeriya yana da daraja saboda dawowar jarin da aka samu bisa la’akari da yawan al’ummarmu sama da miliyan 200 da kuma yawan kasa.
“Shugaban kasa a shirye yake ya tabbatar da cewa mutane sun samu darajar jarinsu, shi kansa hamshakin dan kasuwa ne. Ya na da tarihin nasarori a jihar Legas lokacin da yake gwamna. A yau Legas ta zama daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a Afirka saboda harsashin da ya kafa.”
Sanata Akpabio, ya tabbatar wa maziyartan sa lafiyar jarin su ta hanyar dokoki, inda ya ce, “Ina mai tabbatar muku da cewa Gwamnatin Tarayya za ta yi duk mai yiwuwa na dan Adam wajen kare jarin ku, ta hanyar samar da dokoki masu ba da damar zuba jari da tsaro ga ‘yan kasarta da masu zuba jari na kasashen waje.
Tun da farko, Muhammed Shafiq ya ce ya kasance a majalisar dattawan ne domin taya shugaban majalisar murnar samun nasarar shi a matsayin shugaban majalisar da kuma yi masa fatan alheri.
Sun ce sun zo ne domin taya shi murnar zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban majalisar dattawa da kuma yi maka bayanin a shirye suke na ci gaba da haɗin gwiwa da gwamnati a fannin ma’adanai da noma da kuma madafun iko.
L.N
Leave a Reply