Ruwan sama kamar da bakin kwarya da zaftarewar kasa a babban birnin kasar Ivory Coast, Abidjan, ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 10, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Tara sun kasance a gundumar Yopougon kuma ɗayan yana Cocody-Angre, shugaban hukumar kashe gobara ta soji (GPSM) ya ce.
Zabtarewar kasa biyu a Yopougon da sanyin safiyar Alhamis ta yi sanadiyar mutuwar wasu da jikkata wasu da dama.
A Cocody-Angre wani ya nutse bayan “ruwa ya tafi da shi”, Anicet Bah, kyaftin din GSPM kuma mataimakin shugaban ayyuka,
Ruwan sama kamar da bakin kwarya ba sabon abu ba ne a wannan lokaci a Abidjan, sai dai kamfanin dillancin labaran AFP ya ce a yayin da birnin ke bunkasa gine-ginen ya zama cikin hadari musamman a gundumomin da ba su da wadata.
BBC/L.N
Leave a Reply