Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, zai zama sabon shugaban Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) a yau, inda zai gaji shugaba Umaro Embalo na Guinea Bissau, wanda ya zama shugaban kasar a ranar 4 ga watan Yulin 2022 a taron koli karo na 61 a birnin Accra.
A yau ne za a sanar da jagorancin Tinubu a birnin Bissau a babban taron shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) karo na 63.
Ana gudanar da zaman taro na 63 na hukumomin shugabannin kasashe da na gwamnatoci a Bissau, babban birnin Jamhuriyar Guinea-Bissau.
Leave a Reply