Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Tallafama Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A jihar

13 251

Sama da mutane 300 wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ta shafa a karamar hukumar Katsina dake jihar Katsina arewa maso yammacin najeriya ne suka amfana da tallafin kayan abinchi da wasu kayayyaki domin rage masu radadin da ambaliyar ta haifar ma su

 

Kayayyakin wadanda hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina (SEMA) ta rarraba ga wadanda ibtilain ya shafa sun kuma hada katifu da bokitai da sauran kayayyakin amfanin yau da kullum na cikin gida

 

Da take kaddamar da rabon kayan a birnin Katsina, shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina(SEMA), Hajiya Binta Hussaini Dangani ta bayyana cewa samar da kayayyakin ya biyo bayan faruwar ambaliyar ruwa ya bayan mamakon ruwan sama da ya haifar da asarar dukiyoyi a tsakanin wadanda lamarin ya shafa a cikin birnin Katsina a makon da ya gabata

 

“Sanin kowane a makon da ya gabata a cikin kwaryar birnin Katsina da wasu sassa na jihar nan, wasu al’ummomi sun fuskanci matsalar ambaliyar ruwa da ta haddasa masu rasa matsugunnai da dukiyoyin su, har a wasu wuraren aka samu rahoton rasa rayukan mutane biyu,” shugabar hukumar ta tabbatar.

 

Ta yi nuni da cewa wadanda lamarin ya shafa ne aka tara a wuri guda domin tallafa masu bayan da hukumar da sauran masu ruwa da tsaki suka ishe su a wuraren da lamarin ya shafe su tare da jajanta masu

 

Hajiya Binta Dangani ta bayyana cewa daga cikin wadanda zasu amfana da kayan tallafin akwai mutane 131 daga unguwar Tudun Katsira da mutum 134 daga Sabuwar Unguwa wadanda sun kunshi al’ummomin Koramar Nayalli da Dutsin Amare duk a cikin kwaryar birnin Katsina

 

A lokacin taron an kaddamar da rabon kayan tallafin inda shugabar ta bukaci wadanda suka amfana da suyi amfani da tallafin yadda ya kamata domin rage masu radadin abinda ya same su

 

Wadanda suka halarci taron rabon kayan sun hada da shugaban karamar hukumar Katsina shi da dan majalisar dokoki mai wakiltar karamar hukumar da shugabanin al’ummomi

 

Kazalika taron ya Samu halartar mai taimakama gwamnan jihar akan lamarin yan gudun hijira hadi da sauran masu ruwa da tsaki da daruruwan wadanda suka amfana da tallafin.

 

 

Kamilu Lawal.

13 responses to “Gwamnatin Jihar Katsina Ta Tallafama Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A jihar”

  1. Hello! This post could not be written any better! Reading this post reminds me of my previous room mate! He always kept talking about this. I will forward this page to him. Fairly certain he will have a good read. Thanks for sharing!
    ?????? ??? ???

  2. Записаться к гинекологу спб В ритме современного мегаполиса, такого как Санкт-Петербург, забота о женском здоровье становится приоритетной задачей. Регулярные консультации с гинекологом, профилактические осмотры и своевременная диагностика – залог долголетия и благополучия каждой женщины.

  3. I got this web site from my pal who told me regarding this website and at the moment this time I am browsing this web site and reading very informative posts at this place.
    hafilat recharge

  4. популярная музыка Роп – Русский роп – это больше, чем просто музыка. Это зеркало современной российской души, отражающее её надежды, страхи и мечты. В 2025 году жанр переживает новый виток развития, впитывая в себя элементы других стилей и направлений, становясь всё более разнообразным и эклектичным. Популярная музыка сейчас – это калейдоскоп звуков и образов. Хиты месяца мгновенно взлетают на вершины чартов, но так же быстро и забываются, уступая место новым музыкальным новинкам. 2025 год дарит нам множество талантливых российских исполнителей, каждый из которых вносит свой неповторимый вклад в развитие жанра.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *