Tsaro: Gwamnatin jihar Neja ta baiwa jami’an tsaro motoci kirar Hilux domin kawo karshen matsalar tsaro dake addabar alummar jihar
Gwamnan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Muhammad Bago ya ce gwamnatin shi zata kawo karashen ayyukan ta’addaci a dukkanin fadin jihar nan bada jimawa ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mikawa jami’an tsaro motoci kirar Hilux 20 a gidan gwamnati dake Minna fadar gwamnatin jihar Neja.
Gwamnan Umar Muhammad Bago ya ce tun bayan hawan sa karagar mulkin jahar Neja ya ke fadi tashin ganin ya lalibo bakin zaran magance matsalar ayyukan ta’addaci da Kuma yadda matasa ke cin Karan su ba babbaka a birnin Minna da kewaye domin ganin an sami alumma ta gari.
Gwamnan ya Kara da cewar “gwamnati ta Yi haka ne domin karawa jami’an tsaro kwarin gwiwar cigaba da ayyukan su na kawo karshen matsalar tsaro da jihar ke fama da shi a Yan shekarun nan”.
Har ila yau gwamna Umar Mohammed Bago ya umurci kwamishinan Yan sandan jihar CP Ogundele Ayodeji da ya tabbatar da an Yi anfani da motocin kamar yadda yakamata.
Inda Kuma ya bukaci su da nuna ba Sani ba sabo ga duk Wanda aka kama Yana tada hankali ko Kai hari a dukkanin fadin jihar Neja. Inda ya ce duk Wanda aka kama Yana Saida kayan maye a kwace gidan sa kana a rushe sa domin zama izna ga wadanda ke sun shiga harkar.
A cewar sa Gwamnatin jihar Neja bazata zura Ido tana ganin ayyukan ta’addaci da Kuma shaye shayen da matasa ke Yi a birnin Minna ya kawowa jihar nakasu ba.
A jawabin sa kwamishinan Yan sandan jihar Neja CP Ogundele Ayodeji ya yabawa Gwamnan jihar Umar Muhammad Bago bisa yadda ya jajirce wajan ganin an magance matsalar tsaro dake addabar jihar Neja, inda ya Sha alwashin tashi tsaye domin ganin hakan ya zama tarihi.
A cikin motoci 20 da gwamnatin jihar Neja ta mikwa jami’an tsaro da ta sanyawa suna operation flush rudunar yan sanda jihar zata dauki 12 inda jami’an tsaro farin kaya na DSS da na civil Defense na da biyu biyu kowannan su, inda Kuma kungiyar sintiri ta Vigilante da hukumar yaki da Shan miyagun kwayoyi da Kuma kungiyar maharba ta jihar Neja sun sami mota dai dai kowannan su.
Nura Muhameed.
Leave a Reply