An Bukaci Gwamnati Ta Ba Fifiko Wajen Bunkasa Noma Don Wadata Abinci Da Dogaro Da Kai
Abdulkarim Rabiu
Yayin da majalisar wakilan Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Bola Tinubu na ware Naira Biliyan 500 don tallafawa al’ummar kasa rage radadin cire tallafin man fetun.
Dan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Bakori-Danja daga Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Balarabe Dabai, ya bayyana ce wa domin cimma burin da ake bukata daga shirin samar da tallafin, ya kamata gwamnatin tarayya ta bada fifiko akan zaman lafiya, harkokin noma da kananan sana’o’i domin baiwa manoma damar gudanar da ayyukan noma mai yawa don inganta abinci da dogaro da kai a cikin al’umma.
Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da Muryar Najeriya jim kadan bayan kamala zaman majalisar na ranar Alhamis din nan.
Alhaji Abdullahi Balarabe Dabai, wanda ya yabawa ‘yan Najeriya dangane da hakuri da juriyar da suka yi duk da wahalhalun da suke fuskanta sakamakon cire tallafin, ya kuma tabbatar da cewa majalisar za ta tabbatar da an yi amfani da kudaden da ta hanyoyin da suka dace.
Ya ce domin cimma burin da ake bukata daga shirin samar da tallafin, ya kamata a bada fifiko akan zaman lafiya, harkokin noma da kananan sana’o’i domin baiwa manoma damar gudanar da ayyukan noma mai yawa don inganta abinci da dogaro da kai a cikin al’umma.
Alhaji Abdullahi Dabai, wanda ya nuna damuwarsa kan irin barnar da rashin tsaro ya janyo wa al’umma a sassa da dama na jihar Katsina, ya bayyana jin dadinsa yadda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwar jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da kuma jami’an sunturi suka fara kwana da idanuwansu biyu. .
Akan tsare-tsaren da ya tanadar wa al’ummar mazabarsa kuwa, dan majalisar ya jaddada cewa a matsayinsa na sabon zuwa har yanyo yana Kan koyon yadda za a shirya kudirori da dokoki kan batutuwan da suka shafi rayuwar al’ummarsa tare da gabatar wa majalisa don samar da doka da kuma aiwatar da su.
“Ina da tanadi na musanman da suka shafi al’ummar mazaba ta musanaman ayyukan da za mu gabatar da wadanda za mu sa a cikin kasafinn kudi, wadanda za su taba rayuwar mata da matasa da suka hada da ilimi, tallafi ga masu kananan sana’oi”. In ji Hon. Balarabe Dabai.
Kazalika dan majalisar ya yi kira ga al’umma das u ci gaba da baiwa gwamnti goyan baya kan tsare tsaren da take das u na saboda a sami nasa wajen aiwatar das u. muna kuma kira ga mutane das u tashi tsaye su nemi abin yi kada zauna a ce sai an jira gwamnati ta yi musanman fanni noma da kiwo.
Kazalika, ya kuma yi kira ga al’ummar mazabar sa da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da goyon bayan duk wani yunkuri na inganta rayuwarsu tare da tabbatar musu da kokarinsa na kawo shirye-shiryen Samar da sana’oi da za su yi tasiri kai tsaye a ci gaban rayuwarsu.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply