Take a fresh look at your lifestyle.

AN TSINCI GAWAR WANI JAMI’IN ZABE DA YA BATA A KENYA

0 200

Rundunar ‘yan sanda a Kenya ta ce an gano gawar jami’in zaben, Daniel Musyoka da ya bace bayan zabe a Kenya. Rundunar ‘yan sandan ta ce an gano Daniel Musyoka a kusa da tsaunin Kilimanjaro a kan iyakar kudancin Kenya, mai tazarar kilomita 200 (mil 124) daga sansaninsa da ke Nairobi. Rahoton ya ce ya fita daga wata cibiyar kidayar kuri’u a gabashin Nairobi domin amsa kiran da aka yi masa, kuma ba a sake ganin sa a raye ba. Wasu ‘yan uwansa mata biyu ne suka bayyana gawar, inda suka ce makiyaya ne suka gano gawar kuma yana da tabo na azabtarwa. Hukumar zabe ta tabbatar da bacewar sa a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ta ce ya bace ne a lokacin da yake bakin aiki a wata cibiyar tantance masu kada kuri’a. Wannan dai ya kasance daya daga cikin lokutan zabe mafi lumana a tarihin Kenya, amma bacewar Musyoka a ranar Larabar da ta gabata ya haifar da damuwa game da tsaron jami’an zaben. A halin da ake ciki dai, ‘yan sanda na gudanar da bincike kan bacewarsa da kuma mutuwarsa. Shugaban hukumar zaben, Wafula Chebukati, ya ce an bayyana sunayen wasu ma’aikatan, an kama shi ba bisa ka’ida ba, kuma ya fuskanci tursasawa da tsangwama. Ya ayyana William Ruto ne a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar litinin, yayin da ake ta cece-kuce a cibiyar kirga kuri’un ta kasa.


Community Verified icon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *