Shugaban Najeriya kuma Shugaban Kungiyar ECOWAS, Bola Tinubu, ya ce an yi nazari sosai kan kalubalen tsaro da ake fama da shi a gabar tekun Yamma kuma za a bullo da dabarar da ta dace don magance ta’addanci.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne game da sabon salon da shugabannin ECOWAS suka dauka na magance matsalar rashin tsaro, tare da samun sakamako mai ma’ana, bayan ganawarsa da shugabannin Jamhuriyar Benin, Patrice Talon, Guinea-Bissau, Umaru Sissoco Embalo, da Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum a fadar gwamnati.
”Ba mu da matsala wajen tara kudade. Mun yi imani muna da kayan aikin da za mu yi hakan. Mun yi imanin za mu iya tara kudaden da suka dace don yakar ta’addanci a yankin,” Shugaban ya shaida wa manema labarai.
Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa, shugabannin kasashen yammacin Afirka sun tattauna sosai kan dorewar dimokuradiyya a gabar tekun Yamma da kuma tsara tsarin tunkarar tsaro.
Tun da farko a taron amsa tambayoyi da manema labarai, shugaban hukumar ta ECOWAS, Omar Alieu Touray, ya jaddada aniyar shugabannin na gaggauta mika mulki ga dimokradiyya a Mali, Guinea, da Burkina Faso.
Leave a Reply