Shugaban kasa Muhammadu Buhari, zai kai ziyarar aiki ta yini daya a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda zai mika tutar ranar jin kai ta duniya 2022, da kuma kaddamar da ayyuka a Maiduguri.
Ana sa ran shugaba Buhari a sansanin sojin sama na Maiduguri, inda gwamnan Farfesa Babagana Umara Zulum, zai tarbe bakunci shugaban kasa tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Ana sa ran shugaba Buhari a sansanin sojin sama na Maiduguri, inda gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum zai tarbe shi da wasu manyan jami’an gwamnati.
Shugaban Buhari zai kaddamar da rukunin gidaje malaman dae a Bulumkutu Railway Junction da kaddamar gidaje 500 na sake tsugunar da su a Molai, da kuma kaddamar da tallafin jin kai ga marasa galihu a gidan gwamnati, da dai sauransu.
Aisha Yahaya
Leave a Reply