Take a fresh look at your lifestyle.

Taimakon Cire Tallafin Man Fetur: Kungiyar NLC ta Kogi ta nemi Gwamnatin Jiha ta sa baki

0 93

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, a jihar Kogi, ta bukaci gwamnatin jihar da ta samar da kayan agajin da za su taimaka wajen dakile illar cire tallafin man fetur.

 

Shugaban kungiyar Kwamared Gabriel Amari ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake magana kan irin wahalar da al’ummar jihar ke fuskanta, sakamakon karin farashin man fetur da gwamnatinsa ta yi na cire tallafin gaba daya.

 

 

 

Kwamared Amari ya bayyana cewa, a yayin da Gwamnatin Tarayya ke aikin samar da ababen more rayuwa ga jama’a, akwai bukatar ita ma gwamnatin jihar ta yi kokarin tallafa wa jama’a.

 

Ya bukaci gwamnatin jihar da ta yi koyi da sauran jihohin da suka samar da matakan saukaka wahalhalun tattalin arziki da tallafin ke haifarwa musamman ga shi marasa galihu da na karkara.

 

Shugaban Kwadago ya ci gaba da cewa idan ba a yi wani abu ba, zai yi wuya ma’aikata su kara habaka aiki sakamakon tsadar sufuri da tsadar rayuwa.

 

Ya ce, “An kara farashin man fetur sau biyu; na farko daga N200 zuwa N500 yanzu daga N540 zuwa N617 kowace lita.

 

“Wannan abu ne da ba za a iya jurewa ba saboda mutanenmu ba za su iya sake biyan kudadensu ba, ciyar da ‘ya’yansu da kuma biyan wasu muhimman hakkokin iyali.”

 

 

 

 

Nigerian Post/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *