Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Yobe Ta Rage Tasirin Ambaliyar Ruwa

69 330

Gwamnatin Yobe ta bullo da matakan dakile illolin da ambaliyar ruwa za ta iya haifarwa a yankunan da Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta gano.

 

 

Gwamna Mala Buni ya bayar da wannan tabbacin ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktansa na yada labarai da hulda da manema labarai, Alhaji Mamman Mohammed.

 

Buni ya umurci ma’aikatar ayyuka da muhalli ta jihar da ta tuntubi ofishin sakataren gwamnatin jihar domin daukar matakan da za su rage illar ambaliyar ruwa yadda ya kamata.

 

 

“Dole ne matakan su kasance masu inganci da daidaito don rage ambaliyar ruwa yadda ya kamata da kuma kare al’ummominmu.

 

 

“Gwamnati ta kuduri aniyar samar da kayan aikin da ake bukata da kuma kayan aiki don dakile matsalar,” inji shi.

 

 

Buni ya bukaci jama’a da su baiwa gwamnati hadin kai da shawarwarin kwararru da ake ba su domin tabbatar da tsaron lafiyarsu.

 

 

“Mutanen mu mazauna birane su ma su tallafa wa gwamnati ta hanyar share magudanan ruwa a gaban gidajensu.

 

 

“Ya kamata ku guji yin gine-gine don toshe magudanan ruwa domin kawo cikas da ambaliya a cikin gidajenku da sauran su” Gwamnan ya shawarci.

 

 

Hada garuruwa daban-daban

 

 

Buni ya kuma umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jiha (SEMA) da ta shirya tsaf don tunkarar yiwuwar afkuwar lamarin.

 

 

Kididdiga daga Yobe SEMA ta nuna cewa bala’in ambaliya a shekarar 2022 ya shafi gidaje sama da 31,262 a fadin al’ummomi 255 daga kananan hukumomin 17 na jihar, yayin da aka kwashe hanyoyi 10 da magudanun ruwa da suka hada garuruwa da kauyuka daban-daban a lokacin damina ta bara.

 

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (Nimet) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) sun yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi ciki har da Yobe a lokacin damina ta bana.

 

 

L.N

69 responses to “Gwamnatin Yobe Ta Rage Tasirin Ambaliyar Ruwa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *