Take a fresh look at your lifestyle.

Kasar Gabon ta zabi ‘yan takarar shugaban kasa 19 a zaben watan Agusta

5 115

Hukumar zaben kasar Gabon ta sanar da tantance ‘yan takara 19 da suka hada da shugaban kasar Ali Bongo na yanzu da wasu tsaffin ministoci da dama a zaben shugaban kasa da za a yi a watan gobe.

 

An amince da takarar Bongo duk da ikirarin da ‘yan adawa ke yi na cewa bai cancanci shugabancin kasar ba.

 

Ya yi fama da bugun jini a watan Oktoban 2018 kuma an kai shi Maroko domin jinya.

 

Shugaban Cibiyar Zabe ta Gabon, Michel Stephane Bonda, ya ce a ranar Lahadin da ta gabata ne aka samu bukatu 27 a wa’adin kammala mika takardun tsayawa takara, sannan 19 sun amince da su.

 

Bongo ya hau karagar mulki ne a zaben shekarar 2009 mai cike da cece-kuce bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo kuma ya sake lashe zabe a shekarar 2016.

 

Duka biyun da Bongo ya lashe zaben, ‘yan adawa ne suka yi takun-saka da su, wadanda suka ce ya yi magudi ne.

 

Ya sake tsayawa takara karo na uku bayan ya shafe kusan shekaru 14 yana mulki. Gabon ba ta da iyaka wa’adin tsarin mulki.

 

Ana kallon tsohon ministan ma’adinai Alexandre Barro Chambrier a matsayin babban mai kalubalantar Bongo.

 

Masanin tattalin arziki wanda haifaffen birnin Paris ne a karon farko yana shiga zaben shugaban kasa.

 

Sauran ‘yan takarar sun hada da Pierre-Claver Maganga Moussavou, wanda ya kafa jam’iyyar Social Democratic Party, da Raymond Ndong Sima, tsohon Firayim Minista.

 

Za a fara yakin neman zaben shugaban kasa ne a ranar 11 ga watan Agusta sannan kuma za a kada kuri’a a ranar 26 ga watan Agusta.

 

 

Africanews/L.N

5 responses to “Kasar Gabon ta zabi ‘yan takarar shugaban kasa 19 a zaben watan Agusta”

  1. путь абая 3 том краткое содержание по главам, путь абая 1 том краткое содержание по
    главам цифрландырудың негізгі жетістіктері,
    цифрлық қазақстан бағыттары күн
    батареясы пайдасы, қазақстандағы
    күн батареялары стартап программа, стартапы в казахстане
    2022

  2. порча что это ислам что такое звезды на самом деле мечи 6 таро:
    значение в отношениях, 6 мечей чувства мужчины
    гадание как узнать имя будущего мужа онлайн
    бесплатно кто относится к знаку зодиака водолей

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *