Gwamnatin jihar Kebbi ta fara aikin feshin sinadarai ta iska domin kashe kwarin da ke ci-rani a kananan hukumominta guda uku, Argungu, Bagudo, da Kalgo.
A yayin kaddamar da jirgin, Gwamna Dr Nasiru Idris, wanda shi ne sakataren gwamnatin jihar (SSG), Alhaji Yakubu Bala Tafida, ya ce an yi hakan ne domin tabbatar da samar da abinci a jihar.
A cewarsa, “kwarin, musamman tsuntsayen quelea, sun kasance babbar barazana ga noman hatsi.”
Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta kuduri aniyar yakar duk wata barazana da za ta kawo cikas ga nasarorin da jihar ta samu a fannin noma.
KU KARANTA KUMA: Murar tsuntsaye: Masanin Ya Bukaci Manoman Kaji Da Su Kara Kula Da lafiyar su
L.N
Leave a Reply