Take a fresh look at your lifestyle.

Jami’an tsaron Nijar sun killace fadar shugaban kasa

0 96

Sojoji a Jamhuriyar Nijar sun killace fadar shugaban kasa, da ma wasu ma’aikatu a Yamai babban birnin kasar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

 

Ba a yi harbi ba kuma babu tabbas ko wannan yunkuri ne na masu gadin fadar shugaban kasar na kwace mulki.

 

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, shugaba Mohamed Bazoum na cikin gidansa tare da iyalansa kuma ana tattaunawa.

 

Wata majiya da ba a bayyana sunanta ba ta shaida wa wannan hukumar cewa matakin ya kasance “fuashi ne” da sojoji suka yi.

 

BBC/L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *