Shugabannin ‘yan adawar Kenya sun gudanar da wani shiri na sa ido kan wadanda rikicin ‘yan sanda ya rutsa da su, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 30, sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da kuma kara haraji.
Ana zargin ‘yan sanda da harbin masu zanga-zangar amfani da harsasai masu rai a yankunan da ‘yan adawa ke samun goyon bayan siyasa.
Ma’aikatar ta ce jami’ai guda ya mutu yayin da wasu fiye da 300 suka jikkata a zanga-zangar.
Hotunan da aka nuna a cikin gangamin sun nuna makoki na kunna fitulu, kuka, da kuma wata uwa tana kuka kan mutuwar danta.
“Me ya sa ake taya su murna? Suna kashe mutanensu. Zaluncin ya yi yawa. Ina za mu dosa a matsayin al’umma?” In ji Zamzam Mohammed Chimba, ‘yar majalisa a Kenya.
A cikin makonni uku da suka gabata, zanga-zangar ta bazu a fadin kasar Kenya inda jama’a suka yi ta yin kira ga gwamnatin shugaba William Ruto kan tsadar rayuwa da sabbin haraji da aka sanya mata wadanda suka haddasa tashin farashin man fetur yayin da harajin man fetur ya rubanya daga kashi 8% zuwa 16%.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama sun yi Allah wadai da ‘yan sanda da yin amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga-zangar.
Africanews/L.N
Leave a Reply