Take a fresh look at your lifestyle.

Juyin Mulki: Shugaban Kasar Chadi Ya Dauki Nauyin tattaunawa Da Shugaban Sojojin Nijar

0 83

Shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby ya ba da kansa ya yi magana da shugabannin sojoji a Nijar tare da bayar da rahoto ga shugaban Najeriya Bola Tinubu, shugaban kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka.

A cewar majiyoyin fadar shugaban Najeriya, Deby ya gana da Tinubu ne a gefen taron gaggawa na kungiyar ECOWAS a Abuja babban birnin Najeriya.

“Shugaban kasar Chadi a taron kasashen biyu ya ba da kansa ya je ya tattauna da sojojin Nijar da kuma bayar da rahoto,” wata majiya ta fadar shugaban kasar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A halin da ake ciki shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS sun yi kira da a gaggauta sakin shugaban kasar Mohamed Bazoum a matsayin halastaccen shugaban kasa da gwamnatin Jamhuriyar Nijar.

Karanta kuma: Kungiyar ECOWAS ta bukaci a maido da mulkin dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar, ta kuma kakaba mata takunkumi.

Sun yi wannan kiran ne a wata sanarwa da suka fitar a karshen babban taron koli da aka gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya, ranar Lahadi.

Shugabannin sun kuma yi watsi da duk wani nau’i na yin murabus na shugaba Bazoum tare da ayyana shi a matsayin shugaban kasa daya tilo da kungiyar ECOWAS da Tarayyar Afirka da kuma kasashen duniya suka amince da shi.

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *