Take a fresh look at your lifestyle.

Masu zanga-zanga sun kai hari ofishin jakadancin Faransa a Jamhuriyar Nijar

0 76

An gudanar da zanga-zangar kin jinin Faransa a wajen ofishin jakadancin Faransa da ke Yamai babban birnin Jamhuriyar Nijar a ranar Lahadi bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a makon jiya.

 

Magoya bayan gwamnatin mulkin sojan da suka yi Allah wadai da matakin da Faransa ta dauka biyo bayan juyin mulkin, sun yi maci a kan titunan birnin Yamai suna daga tutocin kasar Rasha tare da rera sunan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin tare da yin tir da kakkausar suka ga tsohuwar mulkin mallaka, Faransa.

 

Gangamin lumana daga baya ta rikide zuwa tashin hankali.

Faransa ta yi Allah-wadai da cin zarafi da ake yi wa ofishin jakadancinta, ta kuma yi alkawarin mayar da martani mai karfi kan duk wani hari da aka kai wa ‘yan kasarta ko muradunta.

 

“Shugaban ba zai amince da duk wani hari da aka kai wa Faransa da muradunta ba,” in ji ofishin Shugaba Emmanuel Macron a cikin wata sanarwa, inda ya bayyana cewa zai mayar da martani ga hare-haren da aka kai wa jami’an diflomasiyyar Faransa, sojojin ko kuma ‘yan kasuwa.

 

Karanta kuma: Majalisar ECOWAS ta yi kira da a kara karfafa tsaro a yankin domin dakile juyin mulki

 

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta yi Allah wadai da duk wani cin zarafi da ake yi wa ofisoshin diflomasiyya tare da yin kira ga mahukuntan Nijar da su kare tawagar Faransa kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanada.

 

Macron ya tattauna da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, sanarwar da ta fito daga ofishin shugaban ta ce dukkansu sun yi Allah wadai da juyin mulkin tare da yin kira da a kwantar da hankula.

 

Faransa wadda tsohuwar mulkin mallaka a Jamhuriyar Nijar ta sanar a ranar Asabar din da ta gabata cewa za ta yanke duk wani taimakon raya kasa da take baiwa kasar tare da yin kira da a mayar da Bazoum kan mukaminsa bayan hambarar da shi da yammacin jiya Laraba.

 

Nijar ta kasance aminiyar tsaro ga Faransa da Amurka, wadanda suka yi amfani da ita a matsayin sansanin yaki da masu tayar da kayar baya a yankin Sahel na yammacin Afirka da tsakiyar Afirka.

 

 

Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *