Take a fresh look at your lifestyle.

Jihar Ebonyi Ta Hada Kai Da Matasa Domin Ci Gaba

0 147

Shugabannin Matasa na Jam’iyyar APC daga kananan Hukumomi 13 na Jihar sun hada gwiwa da mataimaki na musamman ga Gwamnan Jihar Ebonyi kan harkokin Matasa, Mista Eze Paul, domin mayar da Jihar Ebonyi a matsayin Jihohin da aka fi samun zaman lafiya a Najeriya.

Shugabannin Matasan sun kuma bukaci Gwamnatin Jihar ta yi hadin gwiwa da su a fannin horaswa da bita a tsakanin matasan Jihar.

Shugaban kungiyar, Mista Nwancho Uchenna, wanda kuma shi ne shugaban matasan jam’iyyar APC na karamar hukumar Ikwo, ya ce matasan Ebonyi an san su da jajircewa ba wai tashin hankali ba, don haka akwai bukatar a ci gaba da shigar da su cikin dukkan ayyuka da shirye-shiryen Gwamnati.

Shima da yake jawabi yayin ziyarar akwai shugaban matasan jam’iyyar APC na karamar hukumar Ebonyi, Mista Ugo Simon ya ce ziyarar ban girma da suka kai domin fahimtar juna ne da kuma zaman lafiya.

A nasa bangaren, mataimaki na musamman ga gwamna kan wayar da kan matasa Mista Eze Paul ya yi alkawarin daukar matasan a kodayaushe saboda ofishinsa na matasa ne.

Gwamnatin da ke yanzu tana abokantaka ne da matasa, ta amince da daukar ma’aikatan lafiya sama da 400 da 0ver 500 kuma za a dauki su a ma’aikatan gwamnati. Duk wadannan da ma wasu na matasa ne”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *