Gwamnatin Najeriya da Botswana sun bude tattaunawa don zurfafa Damarar zuba jari tsakanin kasashen biyu
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Kungiyar Kasashen Afirka, Kayode Fayemi ne ya bayyana haka ta shafinsa na Twitter.
Extremely productive meeting with His Excellency, President Mokgweetsi Masisi @OfficialMasisi of Botswana in his Gaborone Office on Friday, along with John Olajide, Chairman of Axxess and Cavista Holdings.
We discussed investments in Technology, Agriculture, Infrastructure and… pic.twitter.com/n2d8lgjXO9
— Kayode Fayemi (@kfayemi) August 4, 2023
A wata ganawa da shugaban Botswana, Mokgweetsi Masisi, wanda shi ma ya samu halartar shugaban Axxess da Cavista Holdings. John Olajide, tsohon gwamnan ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa sun tattauna a fannonin zuba jari a sassa daban-daban.
“Mun tattauna batun saka hannun jari a fannin Fasaha, Noma, Samar da ababen more rayuwa da bunkasa jarin dan Adam. Ina matukar fatan ziyara ta gaba. Na gode ya shugaban kasa.”
Idan za a iya tunawa, Shugaba Masisi ya bayyana a cikin wata sanarwa a watan Mayun 2023 ya nuna sha’awar karfafa dangantakar kasashen biyu da Najeriya, bayan mika mulki cikin lumana ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Bayanin hakan ya fito ne a yayin wani taron karawa juna sani da hukumar kula da harkokin Afirka (CCA), da Axxess, da gwamnatin Botswana suka shirya.
Shugaba Masisi ya jaddada mahimmancin inganta dangantakar zamantakewa da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu sun amince da Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da ke kan gaba a fannin tattalin arziki a Afirka.
Ladan Nasidi.
Leave a Reply