Gwamnan jihar Katsina Dr Dikko Umaru Radda, ya jaddada bukatar hada hannu da Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya domin magance matsalolin muhalli a jihar.
Gwamna Radda ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci babban sakatare na ma’aikatar muhalli ta tarayya Alh Ibrahim Yusufu a Abuja ranar Litinin.
Gwaman ya lura cewa muhalli na daya daga cikin muhimman abubuwan da duniya ke mayar da hankali a kai a yanzu a dalilin kalubalen muhallin da duniya ke fuskanta sakamakon sauyin yanayi, zaizayar kasa da kwararowar hamada. Ya kara da cewa wasu daga cikin wadannan kalubalen na matukar shafar jihar.
Dokta Radda ya kara da cewa, kasancewar hakan yana karkashin ikon sakataren dindindin ne da kuma kasancewarsa dan asalin jihar Katsina, ziyarar na neman goyon bayansa ne wajen magance matsalolin muhalli a jihar tare da samar da bayanan da suka wajaba a kan abubuwan da suka shafi muhalli wadanda da jihar zata iya amfana da su.
Gwamnan ya bayyana cewa daga yanzu za a kira taro da daraktocin ma’aikatun tarayya ‘yan asalin jihar Katsina karkashin jagorancin babban sakataren na ma’aikatar Muhallin domin ganin yadda za su taimaka wa jihar daga bangaren su.
Da yake mayar da martani, babban sakatare Alh Ibrahim Yusufu, ya godewa gwamnan bisa samun lokacin da ya kai ziyara ma’aikatar tare da tabbatar masa da kudirin ma’aikatar na yin aiki da gwamnatin jihar Katsina, ya shaidawa gwamnan cewa yana taimakawa jihar a fannoni da dama wandanda suka hada da shirin Ruga na Naira biliyan 6.2 da kuma alfarmar da ake yi wa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da Jami’ar Tarayya dake Dutsinma da dai sauransu.
Alh Yusufu ya kuma ce za a iya cimma nasarori da dama idan suka hada karfi da karfe domin jihar ta amfana da shirye-shiryen gwamnati da dama .
A cewarsa, ya taimaka wa matasa da dama wadanda ‘yan asalin jihar ne ta fuskoki daban-daban, ya kuma tabbatar wa gwamnan cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kara yiwa jihar hidima.
Kazali ya bayyana fatansa cewa idan aka hada hannu za a iya cimma nasarori da dama a jihar.
Abdulkarim Rabiu
Leave a Reply