Take a fresh look at your lifestyle.

Bakin haure 41 ne suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a gabar tekun Italiya

0 143

Wasu bakin haure 41 ne suka mutu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, kamar yadda wasu da suka tsira suka shaida wa kafar yada labaran kasar.

 

Wasu gungun mutane hudu da suka tsira daga bala’in sun shaida wa masu aikin ceto cewa suna cikin wani jirgin ruwa da ya taso daga Sfax na kasar Tunisiya ya nutse a kan hanyarsa ta zuwa Italiya.

 

Fiye da mutane 1,800 ne suka rasa rayukansu a bana a hanyar tsallakawa daga arewacin Afirka zuwa Turai.

 

 

BBC/Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *