Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Yi Alkawarin Yaki Da Rashin Tsaro

0 198

Kungiyar Gwamnonin Kudu Maso Gabas ta kuduri aniyar yaki da tashe-tashen hankula a yankin daidaiku da kuma baki daya, tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodinma, ya yi wannan yabon ne a ranar Alhamis a jihar Enugu, a karshen taron su da suka gudanar a fadar gwamnatin jihar.

A cewar Gwamna Uzodinma, wadanda suka haddasa rashin tsaro a yankin da masu daukar nauyinsu miyagu ne, kuma bai kamata a rika kallonsu a matsayin masu tayar da hankali ba.

Muna yabawa jami’an tsaro bisa hadin kan da suka ba su har ya zuwa yanzu, muna kara musu kwarin gwiwa da kada su yi kasa a gwiwa.

“Saboda haka, idan aka kama, duk wani mutum ko gungun mutanen da aka kama suna aikata wani laifi ya kamata a hukunta su kamar yadda dokar kasa ta tanada,” in ji Uzodinma.

Kungiyar ta kuma yaba da kokarin jami’an tsaro na yaki da miyagun laifuka a yankin.

Kungiyar ta yanke shawarar gudanar da taron tsaro da tattalin arziki a ranar da za a bayyana nan ba da jimawa ba.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Sanata Hope Uzodinma, Gwamnan Jihar Imo (Shugaba); Farfesa Chukwuma Soludo, Gwamnan Jihar Anambra; Dr. Alex Otti, Gwamnan jihar Abia; Francis Nwifuru, Gwamnan Jihar Ebonyi da Dr. Peter Mbah, Gwamnan Jihar Enugu (Mai watsa shiri).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *