Babban hafsan sojin saman Kasar Jamus, Ingo Gerhartz, ya ce Jamus za ta mallaki jirgin sama mai saukar ungulu na biyu mafi girma na NATO tare da 60 Chinooks.
A watan da ya gabata, Jamus ta ce za ta sayi jirage masu saukar ungulu na Chinook 60 daga Boeing (BA.N) a cikin wani kunshin da zai lakume Yuro biliyan 8 (dala biliyan 8.7), gami da muhimman ababen more rayuwa na jirgin.
Gerhartz ya ce “Za mu zama kasa ta biyu mafi girma da helikofta a NATO bayan Amurka.”
Gerhartz ya kara da cewa, kusan jirage masu saukar ungulu na Chinook 50 ne za a jibge a yankin Holzdorf/Schoenewalde da ke gabashin Jamus, inda za a kuma girke karin sojoji 1,000.
“Shafin Schoenewalde zai taka muhimmiyar rawa ga Sojan Sama, da dukan Bundeswehr da tsaron Jamus,” in ji shi.
REUTERS /Ladan Nasidi.
Leave a Reply