Take a fresh look at your lifestyle.

Rundunar Sojin Niger Za Ta gurfanar da Hambararren Shugaban Kasar bisa laifin cin amanar kasa

0 137

A ranar 26 ga watan Yuli ne gwamnatin jamhuriyar Nijar ta ce za ta iya gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum bisa laifin cin amanar kasa.

 

Jagororin juyin mulkin dai sun daure Bazoum a gidan yari tare da rusa gwamnatin da aka zaba, lamarin da ya janyo suka daga manyan kasashen yammacin Afirka, wadanda suka sanya rundunar sojan da ke shirin shiga tsakani don maido da Bazoum.

 

Kanal Amadou Abdramane, mai magana da yawun gwamnatin mulkin sojan ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa, “sun tattara abubuwan da suka dace domin gurfanar da hambararren shugaban bisa laifin cin amanar kasa da kuma kawo cikas ga tsaron ciki da wajen Nijar.”

 

A yau litinin ne ake sa ran babbar kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka za ta kara matsa kaimi wajen tattaunawa da gwamnatin mulkin soji, lamarin da ke nuni da cewa akwai yuwuwar samun matsaya ta diflomasiyya kan takun sakar da ake yi na juyin mulkin.

 

Majalisar dokokin kungiyar a ranar Asabar ta ce zata aike da kwamitin da zai gana da gwamnatin mulkin soja a Yamai.

 

Ba a bayyana lokacin da aka tsara na wannan aikin ba.

 

A yau litinin ake sa ran kwamitin sulhu da tsaro na kungiyar tarayyar Afrika 55 zai gana domin tattauna halin da ake ciki a Nijar, al’amarin da ke nuni da irin yadda ake nuna damuwa kan yuwuwar tabarbarewar juyin mulkin da aka yi a yammacin Afirka na bakwai cikin shekaru uku.

 

Ba wai makomar Nijar mai arzikin Uranium ne kadai ba, kuma kawancen kasashen Yamma a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, har ma da tasirin wasu manyan kasashen duniya masu kishin kasa da ke da manyan muradu a yankin.

 

 

 

Reuters/ Ladan Nasidi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *